A ranar Asabar, 12 ga watan Yuni, 2021, Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya ce zai dabbaka shawarwarin da aka ba shi wajen shawo kan rashin tsaro.
Jaridar Premium Times ta rahoto Gwamnan jihar Zamfara ya na cewa zai yi aiki da rahoton binciken da aka gabatar masa bayan shiga ofis a shekarar 2019.
Bello Matawalle ya kafa wani kwamiti da ya zargi wasu sarakunan gargajiya da hannu dumu-dumu wajen taimaka ‘yan bindiga, aka bada shawarar a tsige su.
Bincike
Tsohon sufetan ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Abubakar, ya binciki abin da ya faru tsakanin watan Yunin 2011 zuwa ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2019.
Rahoton ya ce binciken kwamitin ya nuna cewa ‘yan bindiga sun karbi sama da Naira biliyan uku a matsayin kudin fansa a hannun mutane 3, 672 a wannan lokaci.
A dalilin sace-sace da kashe-kashen, mata 4, 983 sun zama zaurawa, 25, 050 sun zama marayu, mutane 190, 340 aka fatattaka daga inda suke cikin shekara takwas.
Har ila yau, makiyaya sun rasa tumaki 2, 015, tinkiyoyi da akuyoyi 141, da kuma jakai da rakuma 2600.
Shawarar da kwamitin binciken ya bada
Kwamitin ya ba gwamnatin jiha shawara ta karbe duk wasu gonaki da ke labin dabbobi, sannan a kawo dabarun kiwon da za su sa makiyaya suzauna a wuri guda.
IGP Abubakar da kwamitinsa sun bada shawarar a hada-kai da jihohin da ke makwabtaka da jihar Zamfara, domin a gyara duk wasu hanyoyi da ke kan iyaka.
A makon jiya aka ji cewa gwamnatin Zamfara ta dakatar da Sarkin Zurmi, Alhaji Atiku Abubakar Muhammad daga karagasa saboda zargin alaka da ‘yan bindiga.
Gwamna Bello Matawalle ya dauki matakin ne bayan harin da ‘yan bindigar suka kai a kauyen Kadawa da ke masarautar Zurmi inda suka kashe mutane akalla 90.
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari