Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu


An watsar da wata mata mai suna Abibat Kehinde mai shekara 24, a babban asibitin Epe da ke Legas da nauyin bashin sama da N131,000 da ba a biya ba na kudin magani, wata uku bayan ta haifi tagwaye a asibitin. 


Matar ta fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Juma’a a Epe cewa mijin nata ya tsere ne bayan ta haihu a ranar 21 ga watan Maris ba tare da ya biya kudin da zai sa a sallame ta daga asibitin ba. 

Matar tace: “Mijina dan Acaba ne. “Tun bayan da na haifi tagwaye a ranar 21 ga Maris ya bace bat ba a sake jin duriyarsa ba. "Ban shirya wa sake haihuwar da na biyu ba kafin na samu wannan juna biyun; amma Allah ne mafi sani. 

Dan Achaba ya gudu daga asibiti bayan samun labarin matarsa ta haifi ’yan biyu Mahaifiyar tagwayen ta ce ba ta da isasshen abinci da za su ci yayin da jariran kuma suna fama da rashin abubuwan gina jiki tun bayan watsar da ita da mijin ya yi wata uku da suka wuce. 

“Mijina ya ce ba zai iya ciyar da da ko da guda ba, barin ma batun ciyar da ’ya’ya biyu tare da mahaifiyarsu. Sannan ya yi korafi game da makudan kudin jinyar da asibitin ke bin mu gabanin ya tsere. 

“Tunda lokacin da ya fice daga asibitin, bai sake dawo wa ya duba ni da jariran ba har zuwa yau din nan. Ya bar mu a asibiti sannan ya arce,” inji Kehinde. Sai dai ta ce ta yi nasarar biyan N30,000 daga cikin gadon asibitin na N161,000, inda ake bin ta bashin N131,000 da har yanzu ba ta iya biya ba. Matar ta roki hukumomin asibitin da su sallame ta tare da ’yan tagwayen nata. 

Shugabannin Asibitin sun ce sai an biya kashi 90 za'a sallameta Jami’in kula da jin dadin asibitin na Epe, Ayanbisi Rauf, ya tabbatar da cewa mijin matar ya yi watsi da ita da tagwayen nata. 

"Mijin ya yi watsi da ita kimanin wata uku da suka wuce sannan duk kokarin da hukumomin asibitin suka yi domin gano inda yake ya ci tura," inji Rauf. 

Ya ce za a sallami mai jegon ne kawai idan ta biya kashi 90 na adadin kudaden da ake bin ta. 

Source: Legit.ng News 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN