Birnin kebbi: An kama tsoho mai shekara 70 yana aikata fasadi da kananan yara mata 2 a Masallacin Idi da tsakar rana


Hukumar Hisbah a jihar Kebbi ta  kama wani tsoho a Masallacin Idi a unguwar Gesse da ke garin Birnin kebbi mai suna Adamu Wasada dan kimanin shekara 70 yana kokarin aikata ba daidai ba da wasu yara mata kanana da rana tsaka.

Hisbah ta kama wannan tsoho da misalin karfe daya na ranar Litinin 28 ga watan Yuni yayin da yake kokarin mika wa yan matan al'aurarsa domin domin su yi wasa da shi. Mun samo cewa yaran kanana yan mata ne da aka aza wa tallar piya wata kuma wannan tsoho yake labawa yana aikata irin wannan mugun aiki.

Shafin labarai mai zaman kansa na ISYAKU.COM ya samo cewa an dade ana zargin wannan tsoho da aikata irin wannan danyen aiki da rana kiri kiri a cikin duhun itatuwa a Masallacin Idi da ke unguwar Gesse. Dubun Adamu ta cika ne ranar Litinin bayan wasu bayin Allah sun kula da abin da ke faruwa kuma suka sanar da hukumar Hisbah, kuma nan take jami'anta suka isa wajen kuma suka kama Adamu.

Wani abin takaici shi ne wannan tsoho bara yake yi, kenan da sunan Almajiranci, smma yake labawa da wannan Almajiranci yake aikata danyen aiki da ke gurbata tarbiyyan kananan yara mata yan kimanin shekara 8 zuwa 9.

Mai gabatar da kara na yan sanda a gaban Kotun upper sharia ta 3 da ke Gangaren Takalau a garin Birnin kebbi Sgt Faruku Muhammad mai lambar aiki 493010 ya shaida wa Kotu cewa " An gurfanar da Adamu Wasada a gaban wannan Kotu ne bisa tuhumar laifuka guda biyu, hulda da kananan yara da kuma yunkurin aikata lalata da wadannan yara". 

Ya ce "Ranar 28 ga watan shida 2021 da misalin karfe daya na rana, hukumar Hisbah dake jihar Kebbi, inda ta fita yawo domin yin Patrol a cikin gari, inda ta kama Adamu Wasada dashi da wadannan yara a filin Idi da ke nan Birnin kebbi (Mun sakaye sunayen yaran su uku) yaran sun hada da wata yar shiyar Junju a garin Birnin kebbi da wata yar Unguwar Narba. Inda shi Adamu Wasada ya cire wandonshi ya ba yaran alauranshi domin su dinga yi mashi wasa da shi. Sannan  kuma ya yi yunkurin aikata lalata da  wadannan kananan yara".

"Wanda wadannan laifuka da ya


aikata sun saba wa sashe na 235 da kuma 122 na kundin shariar Penal Code na jihar Kebbi bisa wadannan laifuka guda biyu ake tuhumarshi a gaban wannan Kotu" Inji Sgt Faruku.

Sai dai bayan Alkali ya tambayi Adamu Wasada ko ya fahimci zargi da tuhuma da ake yi masa a gaban Kotu ? Adamu ya ce "Eh" sai dai ya musanta tuhumar da ake yi masa.

Kazalika Kotu ta tambayi yaran ainihin abin da ya faru kuma sun yi wa Kotu bayani. Daga bisani Alkalin Kotun ya bayar da umarnin kai yaran gidan adana yara masu laifi Remand Home, ya kuma yi umarnin a kai Adamu Wasada gidan gyara hali da ke garin Birnin kebbi har zuwa ranar Litinin mai zuwa domin ci gaba da shari'ar.

SU WAYE WADANNAN YARA ?

Bayanai da shafin labarai na ISYAKU.COM ya tattaro sun tabbatar cewa kananan yara mata da Adamu ke kokarin gurbata tarbiyyarsu yara ne da aka aza masu tallan piya wata da sauran nau'ukan talla. Mun samo cewa ana zargin ya basu N500 cewa su zubar da ruwan domin su fuskance shi domin biya masa bukata.

DA RANA KIRI KIRI A CIKIN MASALLACIN IDI TSOHON KE AIKATA FASSADI.

Wani abin ban haushi shi ne wannan tsoho mai kimanin fiye da  shekara 70, yana aikata wannan harka ne da rana kiri kiri. An kama shi ne da karfe daya na tsakar rana a cikin ni'imar itatuwa da ke cikin Masallacin Idi a Unguwar Gesse. 

WANNAN TSOHO MABARACI NE MAI BAIYANANNEN HANKALI

Bayanin da muka samu ya nuna cewa wannan tsoho mabaraci ne mai hankali. Kuma marmakin ya amfana da kudin bara da al'umma ke bashi, sai yake amfani da kudin bara da ya samu domin gurbata yayan al'umma da suka taimaka masa da kudin bara domin rayuwarsa ta inganta amma ya dukufa domin gurbata rayuwar yara kanana yan mata.


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN