Bidiyon bikin soja mace, ana kada ganga tare da mika mata takobi


Ba a kowacce rana bace ake ganin bikin sojoji ba. Amma a duk lokacin da aka gani, ana ganinsu cike da aji da kasaita tare da jarumta.

Wani bidiyon sojan Najeriya mace ana shagalin bikin aurenta ya janyo maganganu daga wurin jama'a saboda tsabar kayatarwan da suka yi.

Lallai bikin ya kasaita

A yayin bikin, an ga sojoji sun zo a kungiyance yayin da suka shiga wurin cike da busa da kade-kade.

A daidai wani lokaci yayi bikin, wata soja mace abokiyar aikin amaryar ta tattaka cike da kasaita inda ta isa wurin da amaryar take sanye da kayan sojoji.

Ta mika mata takobi a matsayin girmamawa da karramawa ga amaryar. Sojoji sun jeru a inda mumbarin amaryar yake sannan suka hada kan takubban tare da yin rumfa ga amarya da ango.

Wani mai amfani da suna @khafilmalikbeauty ya wallafa bidiyon a Instagram.

A bidiyo na biyu, an ga lokacin da sojojin suka mika takobi ga amaryar.

Ina son soja nima

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a.

dearbody_abuja cewa tayi: "Nima soja ina so. Allah ya albarkaci gidanta."

maereey__ cewa tayi: "Wayyo sun yi kyau!!!"

mom_nicki cewa tayi: "Tsigar jikina ta tashi. Me yasa ban zama soja kamar haka ba."

A wani labari na daban, Ofishin hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa (EFCC) ta fara bincike kan zargin wasu mutum uku da ake da hada kai wurin cuta tare da buga kudin jabu.

Wadanda ake zargin sun hada da Sylvanus Ireka Ifechukwu, Patrick Chima ibiam da Ajimijere Mathias Adegbenro, Channels TV ta ruwaito.

'Yan sanda na bangaren bincike na musamman dake hedkwatar hukumar ta Obalende, jihar Legas sun yi kamen a ranar 30 ga watan Afirilun 2021 kuma suka mika su gaban EFCC domin cigaba da bincike.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN