Babban zance: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Gidaje a Jiharsa Saboda Masu Garkuwa da Mutane


Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, ya sha alwashin zai rushe duk wani gida da aka gano masu garkuwa suna buya a cikinsa, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Gwamnan yace ba zai yuwu mutanen da suka hana jama'a zaman lafiya kuma ace suna samun wurin ɓoyewa ba.

Gwamna Abiodun ya roƙi al'ummar jihar musamman masu gidajen haya, su tabbatar sun san waɗanda suke baiwa gidajen su.

Gwamnan yayi wannan gargaɗi ne yayin da yake jawabi a wurin wani taron kiristoci karo na 11 a Yewa, jihar Ogun.

Wannan ba shine karon farko da gwamnan Ogun yayi wannan gargaɗi ba na rushe duk wani gida da masu garkuwa ke amfani da shi.

A shekarun baya gwamnan yayi wannan gargaɗi, inda har yayi barazanar kama mamallakin gidan, wanda ya baiwa baragurbi maɓoya a gidansa.

Source: Legit.ng News

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE