Asirin Matar Da Ta Rika Gallaza Wa ‘Ya’yan Kishiyarta Da Horo Da Yunwa Ya Tonu A Bauchi


Wata mata mai suna Habiba Sani Khalid wacce aurenta ya mutu da tsohon mijinta, mazauniyar unguwar Bakin Kura a cikin kwaryar Bauchi ta bankado yadda kishiyarta da ta bari a gidan tsohon mijin take gallaza wa ‘ya’yanta da yunwa da kuma mummunan horo da ya kai ga kassara su.

Malama Habiba, ta ce, daya daga cikin ‘ya’yan nata, mace ‘yar shekara uku mai suna Sumaiya Yakubu kadan ya rage ta tafi barzahu biyo bayan azaba da uwar daki (Kishiyar) take mata tsawon lokaci.

Mahaifiyar yarinyar ta gabatar da korafinta ga ‘yan jarida a asibitin Tashar Babiye da ke garin Bauchi, inda aka kwantar da karamar yarinyar domin jinya.

Ta bayyana cewar, kishiyarta takan hana yaran abincin da za su ci, hadi da yawan duka da take yi masu, “Sannan akwai wata ‘yarta ‘yar shekara 18 da take yawan azaftar da karamar yarinyana ‘yar shekara uku da wuta a gaban uwar ta.”

Habiba ta zayyana cewar, ‘yar tata mai shekaru 18 ta kan dauki garwashin wuta tana kona kanwarta ta Sumaiya  yayin da take tsaftace mata jiki bayan tsuguno akan shadda.

Habiba ta ce, kishiyarta tana yawan dukan ‘ya’yanta Sumaiya Yakubu da wanta Abubakar Yakubu, kuma tana hana su abinci a lokutan da suka dace.

“’Yar kishiyar tawa, tana azabtar da kanwar ta ce Sumaiya a gaban uwarta da kuma ubansu, haka wannan mummunan lamari yake gudana har zuwa lokacin da ya fito a fili”.

Ta ce, “Uban yaran ne wata rana ya kira ni ta wayar tangaraho, ya umarce ni na kwashe yarana. Ya ce idan ban kwashe su ba, ba zai cigaba da kulawa da su ba, domin akwai wasu yaran da yake kulawa da su.

“Ganin na ki kwashe yaran ne, uban su da kansa ya turo mini su. Zuwan su ke da wuya sai na ga ita Sumaiya tana karkarwa, tana ce mun za ta ci abinci. Kuma na ga alamun duka da kuna a jikin ta”.

“Da aka tambaya mene ne ya same ta, yarinya ta zayyana dukkan halin da take ciki. Lamarin da ya sanya ‘yan uwana zubar da hawaye, suka dauki hoton yarinya suka jefa a yanar gizo jama’a suka gani, ya jawo hankalin hukumomin kare ‘yanci wadanda suka zo Bauchi domin kawo wa yarinyar dauki”, In ji Habiba.

Wata mai kare hakkin dan-adam kuma Daraktan Gidauniyar Tallafa wa Mata da Yara ta ‘Syndicate in Supporting Women and Children Initiatibe (SISWACHI)’, Hajiya Binta Adamu Ibrahim, ta ce an umarce ta ne daga shalkwatar su ta Abuja ta shiga cikin wannan lamari da zummar ganin an yi adalci.

Binta ta ce, kungiyar su ta gabatar da lamarin a ofishin ‘yan sanda dake Bauchi, kuma an cafke uban yaran da matar tasa, hadi da babbar ‘yar su mai gallazawa kanwar ta.

Ta bayyana cewar, yaran sun kasance tamkar kwarankwal saboda rashin basu abinci, don haka kungiyar take kula da su

Likitan da aka kawo masa yaran, Mark A. Garba ya ce lokacin da aka kawo su, sun tagayyara amma yanzu lafiyar su ta dan inganta.

Kakakin ‘yan sandan SP Ahmed Mohammed Wakil ya gaskata wannan lamari, ya ce za a gurfanar da masu laifin a gaban kotu.

Rahotun Leadership Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN