An yanke wa uwargida hukuncin daurin watanni 6 bayan kona gidan Amaryar tsohon mijinta


Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Rigasa, Kaduna a ranar Laraba ta yanke wa wata mata ’yar shekara 34,mai suna Zainab Ibrahim, hukuncin daurin watanni shida saboda kona gidan tsohuwar matar tsohon mijinta, rahoton DN.

Alkalin kotun, Salisu Abubakar-Tureta ya yanke wa Zainab hukuncin ne bayan ta amsa laifukan da suka shafi ke ta haddi da barna ta hanyar wuta.

Alkalin ya bai wa mai laifin zabin tarar N10,000.

Mista Abubakar-Tureta ya kuma umarce ta da ta biya N131,000 a matsayin diyyar kone wasu kayayyakin amfani Mallakar Maryam Ramalan.

Tun farkon lamarin, lauya mai shigar da kara, Insp Sambo Maigari ya fada wa kotun cewa laifin ya saba wa Sashi na 174 da 373 na Laifi.

Ya ce mai laifin ta amsa cewa ta yi amfani da fetur ne wajen kona gidan sabuwar amaryar saboda Zafin kishi, riwayar Pulse.

A cikin rokon ta na neman yafiya, ta yi iƙirarin cewa ta kasance mace mai biyayya ga tsohon Mijinta, Har zuwa lokacin da ya sake ta ya auri wata matar.

Ya yi alkawarin dawo da ni gidan aure na amma hakan ya faskara bayan dumbin bauta masa da nayi shi da Iyayensa tsawon shekaru

Ta ce "Gidan Mallakin ta ne ita da yaran ta bakwai."

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN