Yanzu yanzu: Soji sun mamaye Unguwar Oshodi, suna neman wasu yan iska, zirga zirga ya tsaya, duba abin da ya faru


Ana cikin rudani yanzu haka a Oshodi da ke birnin Lagos bayan soji sun mamaye muhimman wurare da ke Unguwar. Lamari da ya tsayar da harkokin zirga zingan jama'a a Unguwar man take.

Yanzu haka fasinjoji da magidanta na nan tsaye ba tare da sanin mafita ba sakamakon dakatar da zirga zirga da lamarin ya haifar.

Jaridar Daily Trust ta labarta cewa sojin sun mamaye Unguwar Oshodi ne da sanyin safiyar Alhamis saboda wasu bata gari sun kashe wani hafsan sojin sama a Unguwar bayan sun yi masa duka har ya mutu.

Jaridar ta ce an barnata motocin bas na jigila da yawa kuma sojin sun lallasa wasu fasinjoji.  

Lamarin ya rutsa da fasinjoji da ke kan hanyarsu ta zuwa wajen aiki yayin da yara yan makaranta suka ranta a na kare suka koma gida domin guje wa tashin hankalin. 

Yanzu haka sojin da ke kai kawo a Unguwar Oshodi suna neman yan iskan da suka kashe hafsan sojin saman a cikin unguwar.

Unguwar Oshodi mahada ce zuwa wasu muhimman unguwanni, kuma nan ne ke da babban tashar motar bas na zirga zirga a Birnin Lagos.

Daily trust ta ce Kakakin hukumar yansandan  jihar Lagos Muyiwa Adejobi, bai amsa kiran wayar salula ba kazalika bai mayar da sakon text da aka yi mata akan lamarin ba.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN