Type Here to Get Search Results !

Yadda mahaifin rikakken dan bindiga ya taka rawa wajen sakin daliban gona a jihar Kaduna


Rahotanni daga majiya mai tushe sun ce tattaunawa kan sakin daliban Kwalejin gona da ilimin gandun daji na tarayya a jihar Kaduna ya gamu da matsala bayan shugaban wadanda suka sace daliban mai suna Buderu ya ki amincewa da sakin daliban duk da yake an biya N15m.

Daily Trust ta Samo cewa ala dole aka jawo mahaifin daya daga cikin rikakken dan bindiga cikin lamarin mai suna Buhari wanda aka fi sani da suna General.

Rahotanni sun ce mahaifin Buhari General ya sa Buhari ya matsa wa Baderu domin ganin an saki daliban. Sai dai  Baderu ya ce idan har ba za a kara biyan wasu kudin fansa ba dole ne a saki wani daginsa mai satan shanaye da aka kama a dajin Falgore a jihar Kano mai suna Laulu wanda sakinsa ya kawo karshen garkuwa da daliban.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Hollywood Movies