Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari


Fasinjoji da dama ciki har da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero sun tsallake rijiya da baya a yayin da jirgin Max Air da ya tashi daga Kano zai tafi Abuja ya samu matsalar inji mintuna 10 bayan tashi daga filin jirgin Kano, MAKIA.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa jirgin na Max Air mai lamba VM1645 wanda ya kamata ya tashi karfe 1.30 na rana amma aka yi jinkiri mintuna 30.

Daga baya jirgin ya tashi misalin karfe 2 na rana da fasinjoji cike maƙil.

An gano cewa jirgin ya fara jigiga a iska kimanin mintuna 10 bayan tashinsa hakan yasa ya yi saukar gaggawa.

Wasu majiyoyi sun ce matsalar inji ne ya janyo lamarin wasu kuma suka ce tsuntsu ne ya yi karo da jirgin.

Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, Dr Sama'ila Suleiman, ɗaya daga cikin fasinjojin da ke jirgin ya ce da ƙyar suka sha yana mai danganta lamarin da sakaci a ɓangaren kamfanin jiragen.

Mr Suleiman ya ce ya ji wani irin sauti na daban a lokacin da jirgin ke tashi amma ya dai bai ce komai ba.

Ya kara da cewa irin wannan firgicin da suka fuskanta ya saka fasinjoji da yawa cikinsu fasa tafiyar suka koma gidajensu.

Kamfanin Max-Air bata ce komai ba game da lamarin har zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoton.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN