Abubakar Malami, antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, ya ce gwamnatin tarayya ta samo sama da dala miliyan 700 a cikin shekaru hudu na daga cikin kudaden da aka wawure.

Ya sanar da hakan ne a ranar Talata a wani taron da aka yi kan shige da ficen kudi ba bisa ka'ida ba da kuma samo su wanda hukumar yaki da rashwa mai zaman kanta (ICPC) ta shirya.

Malami yace kasashen da ke tasowa a Afrika suna rasa sama da $148 biliyan ga rashawa a kowacce shekara, The Cable ta ruwaito.

"Najeriya ta hanyoyin da take bi da kuma hadin kan wasu kasashe, ta samu an dawo da sama da dala miliyan 700 daga Amurka, Ingila, Bailiwick ta Jersey, Switzerland da Ireland a cikin shekaru hudu da suka gabata," yace.

"Har a halin yanzu muna aiki da wasu kasashen ketare domin tabbatar da cewa an dawo da dukkan kadarorin Najeriya dake can."

Malami wanda ya samu wakilcin Juliet Ibekaku-Nwagwu, babban mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin shari'a, ta jajanta yadda manyan kudade ke fita daga Afrika ba bisa ka'ida ba wanda hakan yasa rashin tsaro ke cigaba da tsananta sannan ake rasa cigaba.

"Babu shakka, wannan fitar kudin ke kawo rashin cibiyoyin lafiya da ilimi, talauci da rashin ababen more rayuwa a kasashen Afrika," ya kara da cewa.

Source: Legit.ng