Gwamnan arewa ya sallami malaman makaranta 20 kan wani muhimmin dalili


Hukumar kula da makarantun frimare ta jiha, SUBEB, ta jihar Niger ta kori malaman makarantun frimare 20 a sassan jihar daga aiki saboda satifiket É—in bogi da rashin zuwa aiki.

A cewar kamfanin dillancin labarai, NAN, an sanar da korar su ne cikin wata sanarwa da Idris Kolo, kakakin SUBEB, ya fitar a ranar Litinin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Idris Adamu, Shugaban SUBEB na Niger, ya ce an kori malamai huÉ—u daga Gbako, sai uku-uku daga Bida da Lapai.

Ya kuma ce an sallami biyu daga aiki a ƙananan hukumomin Agaie, Katcha da Lavun yayin da aka sallami mutum ɗai-ɗai a ƙananan hukumomin Mashegu, Munya da Shiroro. Ya kuma ce an kori malami ɗaya a Kontagora saboda rashin zuwa aiki.

"Hukumar ta yanke shawarar korar dukkan malaman da ba su cancanta ba a makarantun frimare a matsayin wani mataki na inganta koyarwa da karantarwa a makarantun frimare na jihar," in ji shi.

Shugaban na SUBEB ya ce hukumar tana mataki na farko na tantance ma'aikata ne kuma za ta cigaba da fatattakar É“ara-gurbi daga cikin ma'aikatan.

Source: Legit.ng News

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN