Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ƙara wa malaman Kano shekarun aiki da shekarun da ya kamata su yi ritaya.
Gwamnan a cikin sanarwar da ofishinsa ya fitar, ya ƙarawa malaman jihar shekaru biyar na aiki daga shekara 35 zuwa 40, haka ma shekarun ritaya daga 60 zuwa 65.
Gwamnan ya sanar da matakin a wani bikin karramawa na ƙungiyar ƙwadago NLC a albarkacin bikin ranar ma’aikata da aka yi a ranar Asabar 1 ga watan Mayu.
Gwamnan na Kano ya ce ya ɗauki matakin ne kan abin da ya kira “ƙarfafa malama da kuma ilimi da ci gaba mai ɗorewa
Matakin ya shafi dukkanin malaman firamare da sakandare da na gaba da sakandare.
A wasu ƙasashe na duniya ma’aikata kan yi zanga-zanga kan tsawaita wa’adin shekarun ritaya ko na aiki.
Rahotun BBC Hausa
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari