Yan'uwan wani mamaci sun dambace a gefen Kabarinsa har wasu suka fada a cikin Kabarin yayin da gawarsa take ajiye a gefe kafin a sakata a Kabari,
Cacan baki ya kaure tsakanin yan'uwan mamacin, daga bisani aka fara damutsa har da dukan juna yayin da gawar mamacin ke ajiye a gefen Kabarinsa kafin a saka shi a ciki.
Faifen bidiyo ya nuna yadda yanuwan mamacin suka dinga yarba wa juna zafafan kalamai, daga bisani an gan yadda suka kaure da dambe har wasu suka fada cikin Kabarin dan'uwansu.
Har ila yau bidiyon ya nuna yadda wani fusataccen dan'uwan mamacin ya dauko Shebur shi ma ya fada cikin Kabarin ya dinga dukan sauran yan'uwan mamacin yayin da muryar wata mace ke furta Allah wadai da yare.
Mun samo cewa Lamarin ya faru ne a kasar Cameroon.
Kalli bidiyo:
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari