Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da fasahar 5G


Daga bisani, cece-kucen da ke tattare da fasahar 5G ta zo karshe bayan gwamnatin tarayya ta kammala shirin rungumar fasahar.

Wannan ya biyo bayan saka hannu kan wata yarjejeniya tsakanin hukumar sadarwa ta kasa (NCC) a ranar Laraba da kuma hukumar sadarwa ta tauraron dan Adam (Nigcomsat).

Vanguard ta ruwaito cewa, a karkashin yarjejeniyar, NIGOSAT zata zuba 160Megs na C-Band wanda gwamnati za ta samu kudin shiga daga siyar dashi ga kamfanonin sadarwa ta karkashin NCC.

Yarjejeniyar kamar yadda mataimakin shugaban NCC, Farfesa Umar Danbatta, ta samu sa albarkar National Frequency Management Council, wanda ya samu shugabancin Ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami.

A bangaren cece-kucen dake tattare da fasahar 5G, EVC tace tuni ta yi bincike a bangaren tsaro da kuma lafiya kuma hukumar ta bazama wurin wayarwa jama'a kai.

Tun dai a farkon 2020 ne maganar fasahar 5G ta janyo cece-kuce a kasar nan.

Source: Legit News


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN