Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa wasu Malaman addini da tsaffin yan siyasa na kokarin hada baki da wasu yan bakin haure wajen yiwa gwamnatin Buhari juyin mulki.
Fadar shugaban kasan ta ce an samu hujjoji kan shirin da ake yi na hada baki da wasu shugabannin kabilu da yan siyasa wajen alanta rashin imaninsu da shugaba Buhari.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.
"Wani shiri da wasu Malaman addini da tsaffin shugabanni ke yi, ana niyyar jefa kasar cikin rudani da rikici, wanda hakan zai tilasta yin juyin mulki," jawabin yace.
"Wasu karin hujjoji sun bauuana cewa wadannan mutanen yanzu haka na kokarin shawo kan shugabannin wasu kabilu da yan siyasa a kafin tarayya, da niyyar shirya wani taro inda za'a nuna rashin amincewa da shugaban kasa, wanda hakan zai jefa kasar cikin rikici."
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari