An kama wani matashi bayan ya saci Plantain a gonar mutane domin ya biya wa budurwarsa bukata.
An kama saurayin ne ranar Litin a wani gona a garin Ebedebiri, da ke karamar hukumar Sagbama a jihar Bayelsa.
Ya gaya wa shugabannin matasa lokacin da ake yi masa tambayoyi cewa ya sato plantain ne saboda budurwarsa ta bukaci ya bata N10.000 domin ta yi kitso da kwalliya. Ya ce ta bashi wa'adi domin ya kawo mata kudin shi ya sa ya je ya sato plantain domin ya sayar ya kai mata kudin.
Sai dai masana sun yi hasashen cewa kaso 80 na sace sace da aikata miyagun ayyuka da wasu matasa ke yi, suna yi ne domin su biya wa yan matansu bukata ko su birge su.
Kazalika masana sun yi nuni da mutuwan zuci ga matasa, kasancewa daya daga cikin dalilan da ke sa su yi sata.
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari