Hukumar yan sandan jihar Nasarawa ta damke mai baiwa gwamna Abdullahi Sule shawara kan ayyukan alfanu da wasu mutum 16 kan laifin sace karafunan layin dogon jirgin kasa.
An damke wadannan mutane ne suna satan karafunan dake garin Lafiya da karamar hukumar Keana na jihar.
Kwamishinan yan sanda CP Bola Longe, ya bayyana hakan ranar Alhamis a Lafiya, inda ya bayyana mutanen.
Ya yi bayanin cewa mutanen da ake tuhuman sun kasance suna kasuwancin sayan karafunan layin dogo daga wajen barayi amma dubunsu ya cika yayinda yan sanda suka samu labari.
"Hukumar yan sanda ta cika hannu da malalata yayinda suke satan karafunan layin dogo a Agyaragu dake karamar hukumar Lafiya da kuma Anguwan Alago dake karamar hukumar Keana," yace.
Yayinda Jaridar Punch taji ta bakin hadimin gwamnan, ya yi bayanin cewa bai san kayan sata ake sayar masa ba.
Yace: "Ni dan kasuwa ne. Ina da dillali mai kawo min kaya kuma na yadda da shi. Ya rasu yanzu.... Wannan shine karo na farko da suka kawo min karafunan layin dogo. Bayan da na saya, na sayar N3.6 million."
Daga cikin wadanda aka damke akwai jami'an yan sanda 2, jami'in NSCDC 1, tsohon Kansila 1 da kuma wani dan kasar Sin.
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari