Magidanci ya kashe Liman bisa zargin kwanciya da amaryarsa


Rundunar yansandan jihar Niger ta kama wani magidanci mai suna Umar Jibril wanda aka fi sani da suna "ba dama" bisa zargin kashe babban Limami na Edati ta hanyar amfani da karfe sakamakon zargin da ya yi wa Liman da kwanciya da Amaryarsa. Kamar yadda isyaku.com ya ruwaito.

Yayin tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin yansandan jihar Niger Adamu Usman ya ce wanda ake zargi ya aikata laifin ne ranar Litinin 12 ga watan Aprilu.

Ya ce wanda ake zargin ya gaya wa yansanda lokacin bincike cewa Limamin yana zina da matarsa. Ya ce ranar da lamarin ya faru da yamma, yana hutawa a kofar gidansa, sai ya gan Liman ya wuce shi ya bi ta gidan makwabcinsa.

Ya ce a daidai wannan lokaci Amaryarsa mai suna Aishatu Umar ta fito ta ce za ta je ta yi bahaya a gefen gidansu. Amma bayan ya jira har tsawon wani lokaci bata dawo ba, sai ya zagaya nemanta. Daga bisani sai ya ji muryarta a gidan makwabcinsa.

"Na shiga daki na sami Liman tsirara kwance a kan gado tare da Amarya ta. Suna barci tare, ban yi komai ba sai na fita daga cikin dakin. Na tafi gidan dan uwa na sai na gaya masa abin da na gani". A cewar Umar.

Ya ce ya kasa rike fushi da bacin ransa ne bayan Liman ya kira shi domin su yi sulhu a kan matsalar.

"A lokacin da muke tattaunawa kan matsalar da Liman, lamarin ya yi zafi, mun yi zafafan muhawwara da juna, sakamakon haka na kwace wani karfen rodi daga hannun Alhaji Hassan sai na caka wa Liman a wuya" Inji Umar.

Shugaban yansandan jihar Niger ya ce za su gurfanar da Umar a gaban Kotu ba tare da bata lokaci ba.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN