Hotuna, sunayen mutane da aka yi wa kisar gilla a Birnin kebbi, ina dalili ?


Ana zargin cewa mutane shida ne aka kashe a garin Birnin kebbi daga ranar 9/11/2019 zuwa ranar 9/3/2021. Akasari an yi wa mutanen kisan gilla ne a gidajensu da dare, kuma bisa ga alamu har yanzu ba a kama wadanda suka kashe wadannan bayin Allah ba.

Gwamnatin jihar Kebbi karkashin shugabancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, tana kokarinta wajen bayar da taimakon kudade da kayan aiki ga jami'an tsaro domin inganta harkar tsaro a jihar Kebbi.

Sai dai tun bayan kisan gilla da ya fara daukan hankalin jama'a da ya faru shekaru da suka gabata, inda aka kashe wata matar aure da wasu yara, aka yi wa gawakinsu gunduwa-gunduwa a gidan mijinta da ke Unguwar Bayan Kara a garin Birnin kebbi.

Har ila yau babu wani bayani daga hukumomi kan ko wa ya aikata wannan aiki. Wannan shi ne matakin farko kuma mabudin ci gaba da aikata kashe kashen bayin Allah a garin Birnin kebbi daga lokaci zuwa lokaci.
Hauwa

1. Aranar 9/11/2019 an tsinci gawar wata budurwa mai suna Hauwa a gidajen bayan Sakatariyar Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi.
Ngozi (Helen)

2. An kashe wata mata mai suna Njoku Rose Ngozi wacce aka fi sani da suna Helen, a B-Joy da ke Unguwar Badariya a garin Birnin kebbi ranar 30/9/2020.

3. A makon farko na watan Oktoba 2020, an tsinci gawar wani mutum wanda ta fara rubewa a yankin Chochi a Unguwar Badariya da ke garin Birnin kebbi.
Isaac (K.I)

4. Ranar 14/9/2020 an raunata Adekusibe Olusola Isaac da makami a gidansa da ke Unguwar Badariya. Ya mutu ranar 16/9/2020.
Kwarangwam

5. An tsinci Kwarangwam na kan Dan Adam a Unguwar Malala da ke Birnin kebbi. Ana zargin Kwarangwam kan wata yarinya da ta bace ne yan makonni a Unguwar mai suna Wasila Bala Mai Tiles ranar 2/2/2021.
Abubakar Tari

6. Ranar 9/3/2021 ana zargin an kashe wani Limami kuma ma'aikacin Asibiti, mai suna Abubakar Zaki Tari a gidansa da ke unguwar Bayan Kara a cikin garin Birnin kebbi.

Bayan wadannan kashe kashe, hakan na ci gaba da haifar da fargaba a zukatan al'umma a garin Birnin kebbi da kewaye. 

Muhammad Salim magidanci ne a garin Birnin kebbi, ya ce "Gaskiya Ina cikin fargaba a ko da yaushe a gidana matukar dare ya yi. Domin ganin cewa har yanzu ba a kama daya daga cikin wadanda suke bin dare suna aikata irin wannan kashe kashe ba a garin Birnin kebbi. Lamarin na da ban tsoro. Allah ne kawai gatan talaka, Ina rokonsa ya kare mu gaba daya daga irin wadannan mutane" 

Sai dai wata majiya ta tsaro a jihar Kebbi ta tabbatar mana cewa za ta fuskanci lamarin kai tsaye tare da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a jihar Kebbi.

Jihar Kebbi da ta shahara a Najeriya wajen zaman lafiya tare da bin doka da oda, ta tsunduma cikin manya manyan matsalolin tsaro da suka hada da sace mutane don karban kudin fansa.

Matsalar Yan daban daji da suka addabi karamar hukumar Danko-Wasagu da Masarautar Zuru. Da kuma barayin shanu da ke kora shanayen bayin Allah a kauyukan Masarautar. Lamari da ya kara tsunduma al'umomin yankin cikin talauci bayan sace masu shanaye da suka dogara da su wajen kiwo domin sayarwa a biya bukatun kudade idan matsalar hakan ta taso.

Sai kuma kashe kashen bayin Allah da ke gudana lokaci zuwa lokaci a cikin garin Birnin kebbi.

Ko miye Gwamnatin jihar Kebbi ke shirin yi domin ganin irin wadannan kashe kashe basu sake faruwa ba a cikin garin Birnin kebbi, duba da cewa manyan jami'an tsaro na rundunonin tsaro na Tarayya, da ofishinsu suna a garin Birnin kebbi ?.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN