Wahayin Fasto: Yar shekara 30 ta kashe mahaifiyarta da adda


Rundunar yan sanda na jihar Ondo ta kama wata mata, Blessing Jimoh, mai shekaru 30 saboda kashe mahiyarta, Ijeoma Odo The Nation ta ruwaito.

Jaridar legit ta ruwaito cewa Blessing ta ce ta halaka mahaifiyarta da adda bayan fasto ya fada mata cewa mahaifiyar mayya ce.

An yi holen ta tare da wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

An ce faston yanzu ya tsere don gudun kada hukuma ta damko shi.

Blessing ta ce tana yara hudu kuma ta aikata laifin ne a lokacin da suke aiki tare a gona a Ile-Iluji.

Ta yi ikirarin cewa hankalinta ya gushe a lokacin da ta aikata laifin.

A cewarta, "Wani abu ne da ke damu na ya saka ni na kashe mahaifiya ta. Ban yi farin cikin abin da na aikata ba.

"Na yanka wutan ta da adda. Fasto ne ya fada min ita mayya ce kuma na tafi in roke ta. Mahaifiya ta yar asalin jihar Enugu ne. Muna ta neman faston amma ba mu gan shi ba."

Kwamishinan yan sanda na jihar Ondo, Bolaji Salami, ya ce za a gurfanar da wacce ake zargin nan bada dadewa ba.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN