Yan bindiga sun farmaki Hanyar Dan layi a garin Bena da ke karamar hukumar Danko-Wasagu da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi suka kora shanaye fiye da 100. Sai dai wata majiya mai tushe a bangaren mahukunta a jihar Kebbi ta ce shanaye 25 ne Yan bindigan suka yi awon gaba da su.
Majiyarmu ta ce da misalin karfe 12 na daren Lahadi 7 ga watan Maris yan bindigan suka dira garin Bena, suka dinga harbin bindiga a cikin iska suna fura usir kuma suna kuwa suna neman a zo a fuskance su.
Majiyar ta ce sun yi nassarar ficewa da shanaye kimanin 100 bayan musanyar wuta tsakanin su da jami'an tsaro tare da jama'an gari.
Kazalika mun samo cewa ba a rasa rai ba a harin na Lahadi bisa rahotun farko da ke fitowa dangane da lamarin.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari