A kasheta kawai, Mahaifin Amaryar da Kishiyarta ta bankawa wuta ya bukaci hukuma


Mahaifin matar da kishiyarta hallaka ta hanyar banka mata wuta ya bukaci hukumomi su tabbatar da cewa an kashe wacce aka kama da wannan laifi. Jaridar legit ta ruwaito.

Malam Ibrahim Yayaha Sidi Na Khalifa ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da Daily Trust.

Ya ce abinda yake so kawai shine a yanke mata hukuncin da ya kamata.

Ya ce a addinin Musulunci, babu laifi idan mutumin da aka zalunta ya zabi daukar fansa saboda Al-Qur'ani ya bayyana hukuncin kisa ba tare da hakki ba.

"Ba zan taba yafe jinin diyata ba. Qur'an yace ' Mun hukunta cewa rai ga rai'.... saboda haka ina son ganin an yanke hukunci kan wadanda suka aikata wannan abin takaicin," Yace.

"Ba zan taba yafe musu ba. Ba hadari bane ko kuskure. Ki bugi diyata har lahira, sannan ki bankawa gawarta wuta, ba zan taba yafewa ba."


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN