Kwamishinan yansandan jihar Oyo Mrs Ngozi Onadeko, ta shaida wa manema labarai cewa ranar Alhamis da ta gabata iyayen yarinyar sun aike ta domin ta sayo Akamu. Amma sai Oladiti ya biyo ta ya dinga lallashinta har ya bata lemun kwalba ta sha, daga bisani sai ta dinga jin barci, bayan ta farka daga barci ne kawai sai ta gan kanta kwance tsirara a kan gadon Oladiti jini yana fitowa daga alaurarta.
Binciken Asibiti ya nuna yarinyar tana dauke da juna biyu na tsawon makonni 29.
Yansanda na ci gaba da bincike, yayin da aka tsare wanda ake zargi, wanda ya gaya wa yansanda cewa shi Lauya ne.
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari