Kashe yan Arewa a Oyo: Bagudu ya jagoranci Gwamnonin Arewa 3 zuwa Oyo , duba abin da zai faru


Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu tare da Gwamnonin jihohin Arewa guda uku sun dira jihar Oyo domin samun mafita kan matsalar tsaro da ya rutsa da yan Arewa a garin Shasha na jihar Oyo.

Gwamnonin da suka hada da Gwamnan jihar Kano Abubakar Ganduje, Gwamnan jihar Niger Abubakar Bello, da Zamfara Bello Matawalle. Gwamnonin sun shiga taron sirri tare da Gwamnan jihar Oyo Mr Makinde cikin dare ranar Litinin 15/2/2021..

Ana kyautata zaton Gwamnonin za su ziyarci wuraren da lamarin ya faru, daga bisani za su zauna tare da masu ruwa da tsaki domin samun mafita kan matsalar tsaro da ya faru tsakanin Yarbawa da Hausawa, tare da nemo hanyar hana sake faruwar lamarin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN