Abin mamaki wata mata ta haifi tagwaye masu mabanbantan launi

Mahaifiyar wasu yara tagwaye a kasar London Kayleigh Okotie tana rayuwa cikin mafarki jaridar legit ta ruwaito.

Matashiyar mai shekaru 32 tana matukar alfahari da yadda tagwayenta suke da kyau da kuma yadda babu kama tsakanin jariran biyu.

Mahaifiyar da abokin tarayyarta Jordan King sun yi maraba da yaransu kuma sun lura cewa jariran suna da kamanni na musamman waɗanda ba kasafai suke faruwa a cikin yawancin tagwaye ba.

Na farko, suna da launuka daban-daban. Dayansu na da launi mai haske yayin da ɗayan ya kasance mai duhu, launin cakuleti.

Masana kimiyya suna kiran abin da ya faru a matsayin "genetic quirk."


Gashin Jaziyah mikakke ne yayin da na Naylah yana da duhu kuma murdadde.

Kayleigh ta gaya wa jaridar The Sun:

"Suna da kamanni daban-daban, abin birgewa ne a gani."

Mahaifiyar 'yan biyun ta nace cewa duk da cewa an haifi yaron da yarinyar a rana ɗaya, kamanninsu kamar na dare ne da rana.

Matashiyar mai shekaru 32 'yar asalin Turai da Najeriya ce amma har yanzu tana mamaki lokacin da ta ga jariran nata a karon farko.

Ta jima tana zazzafan nakuda, ta bayyana abinda ta iya yi bayan ta haifi yaran shine rungume yaran da yin bacci.

Lokacin da ta farka, Kayleigh ta lura cewa ta rasa cikakken bayani game da jariran nata.

Awani labarin, Kafin haihuwar 'yan hudun a ranar Juma'a, 5 ga watan Yuni, Hauwa'u ta haifi yara 13 a baya.

Yayin hirarta da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Talata, Hauwa'u ta ce yanzu tana da 'ya'ya 17 daga haihuwa takwas da ta taba yi.

An mayar da Hauwa'u da jariranta zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zaria domin samun kyakyawar kulawa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN