Yan bindiga sun yi awon gaba da yan sanda 18 a jihar Kaduna


Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da jami'an yan sanda 18 a Farin-Ruwa, hanyar Birnin Gwari - Funtua a jihar Kaduna, Arewa masi yammacin Najeriya.

SaharaReporters ta ruwaito cewa yan sandan na hanyarsu ta zuwa Kano daga Minna, jihar Neja ranar Juma'a.

Amma majiyoyi sun bayyana cewa Sojoji sun ceto kimanin yan sanda 10 a Maganda ranar Asabar.

Shugaban kungiyar cigaban Birnin Gwari (BEPU), Barista Salisu Haruna, ya tabbatar da harin a wani jawabi.

Haruna ya ce yan sandan dake Dogon Dawa sun samu labarin hakan.

Yace, "Kungiyar cigaban Birnin Gwari (BEPU) ta ruwaito cewa har yanzu ba'a san idan jami'an yan sanda 18 da aka kaiwa hari a hanyar Birnin-Gwari Funtuai ranar Juma'a, 15 ga watan Junairu, 2021, suke ba.

"Yan sandan 18, wadanda ke kula da hanyar Birnin Gwari Funtua, an gamu da hari ranar Juma'a. A lokacin da ake kawo wannan rahoto, bamu san adadin wadanda abin ya shafa ba."

"Masu idanuwan shaida na tunanin wasu cikin yan sandan sun rasa rayukansa yayinda sun bace cikin daji."

"Rahotannin sun tabbatar da cewa yan sanda biyu sun yi waya domin sanar da gida cewa an kai musu hari amma basu san inda suke ba."

"BEPU na kira ga gwamnati, wacce aka saurawa hakkin kula da rayukanmu da dukiyoyinmu, ta mike tsaye domin yaki da rashin tsaro har sai an samu nasara."

A wani labarin daban, rundunar Sojin Najeriya sun kashe wasu yan bindiga a harin da aka kai musu a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Aruwan ya ce rundunar mayakan sama sun hallaka yan bindiga da dama kan baburansu a Saulawa, Kuduru da Farin Ruwa.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN