Kwastam ta gano alburusai 5,200 da aka boye cikin wasu kaya, kudinsu ya haura N378m


Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wacce aka fi sani da Kwastam ta sanar da kama alburusai da wasu haramtattun kaya da kudinsu ya kama Naira miliyan dari uku da saba'in da takwas da dubu dari bakwai da hamsin da daya da dari tara da talatin da biyar (N378,751,35.00).

Reshen hukumar na Owerri ne ya sanar da cewa ya kama alburusan da sauran kayan a tsakanin watan Nuwamba zuwa Disamba na shekarar 2020, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Yayin da yake sanar da hakan, shugaban ofishin yankin, Kwantirola Yusuf Lawal Psc(+), ya bayyana damuwarsa akan yawaitar safarar makamai.

Ya bayar da misalin yadda aka kama dumbin makamai a Lagos a shekarar 2017, a Kwara a shekarar 2018, da kuma baya bayan nan a Jihar Kebbi.

Ya kara da cewa duk da haka, sai gashi an sake kama wata mota da ke dauke da alburusai 5,200 a ranar 13 ga watan Disamba na shekarar 2020.

A cewar Lawal, an kama motar ne a hanyar Nwezenyi zuwa Ikom ta jihar Kuros Riba bayan samun sahihan bayanan sirri akan yadda aka boye alburusan a cikin sauran wasu kayan amfanin gida.

"Allah ne kadai yasan abinda zai faru da wadannan alburusai sun kai wurin da aka yi niyya, musamman yadda ake fama da matsalar garkuwa da mutane da fashi da makami da matsalar 'yan bindiga," a cewarsa.

A wani labarin, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa fadar shugaban kasa ta yi raddi tare da yi wa jam'iyyar adawa ta PDP kaca-kaca.

A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami'ar karya, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

A cewar fafa shugaban kasa, jam'iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN