Wani likita ya kamu da kwayar cutar korona sati daya bayan allurar rigakafi


Wani likita ya kamu da kwayar cutar korona sati daya bayan allurar rigakafi

Wani likita da ke aiki a wani asibiti a Jih okar California ta kasar Amurka ya kamu da kwayar cutar korona sati daya bayan yi masa allurar rigakafi.

Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa an yi likitan allurar rigakafi ta kamfanin Pfizer a makon da ya gabata.

Sakamakon faruwar hakan, kamfanin Pfizer ya bayyana cewa cigaba da bibiyar dukkan wasu bayanai dangane da sabuwar allurar rigakafin.

"Rigakafin na bukatar lokaci kafin ta ginu a jikin mutum, mutum zai iya kamuwa da kwayar cutar kwanaki goma kafin ko bayan yi masa allurar rigakafin," a cewar wata sanarwa da kamfanin ya fitar.

A ranar 18 ga watan Disamba ne likitan mai suna Matthew W., dan shekaru 45, ya sanar da cewa an yi masa allurar rigakafin korona ta kamfanin Pfizer.

A lokacin, Matthew ya bayyana cewa bayan ciwon wuni guda da hannunsa ya yi, allurar ba ta da wata illa.

A ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba, ne Legit.ng ta rawaito cewa cutar korona ta hallaka tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a mulkin soji, Air Commodore Idongesit Nkanga.

Kafin rasuwarsa, Nkanga shine shugaban kungiyar kishi da son cigaban yankin Neja-Delta (PANDEF)

Marigayi Nkanga ya shugabanci jihar Akwa Ibom daga shekarar 1990 zuwa shekarar 1992 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN