Uwar jam'iyyar APC ta soke dakatarwar da aka yi wa Ameachi, ta yi barazanar hukunci


Kwamitin rikon kwarya na na kasa na jam'iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, a ranar Laraba, ta soke dakatarwar da aka ce an yi wa Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi da wasu mambobin APC a Jihar Rivers, The Punch ta ruwaito.

Tsagin jam'iyyar APC masu yi wa Igo Aguma biyayya a Rivers ta sanar da dakatar da Ameachi, Sanata Andrew Uchendu da tsohon mataimakin sakataren APC na kasa, Victor Giadom kan zargin cin amanar jam'iyyar.

Uwar jam'iyyar ta aike da wasika ga jam'iyyar reshen Jihar Rivers game da dakatar da su Ameachi ga Igo Aguma inda ta gargadi tsaginsa ta dena aikata wani abu da zai iya kawo tashin hankali a jam'iyyar.

Shugabannin jam'iyyar na kasa sun ce suna bukatar lokaci don yin bincike kan jan hankalinsu cewa akwai wasu da ke ikirarin su shugabanin jam'iyyar ne a matakin mazabu.

Wani sashi na wasikar ya ce, "Mun duba sunayen da muka da shi na shugabannin jam'iyyar a sakatariya kuma mun gano wadannan mutanen ba sune shugabannin jam'iyya a Rivers ba.

"Don haka, an shugaban jam'iyya, Mai girma, Gwamna Mai Mala Buni, ya umurce ni in sanar da kai cewa Hon. Isaac Ogbobula ne shugaban APC na Jihar Rivers da aka rantsar a sakatariyar kasa da Disamban 2020 yayin taron shugabannin jam'iyya da aka yi a Aso Rock, Abuja."

Wasikar ta kara da cewa, "Ina son janyo hankalinka da sauran mambobin APC na Jihar Rivers game da hukuncin da kundin tsarin mulkin jam'iyya da na kasa suka tanada ga masu yin sojan gona."

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN