Matawalle ya fadi sirrin yin galaba kan yan bindiga a Arewa


Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya ce lalata dukkanin sansanin 'yan bindiga da ke Jihar Zamfara ne zai kawo karshen hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa a Arewa maso Yammacin kasar.

Matawalle ya yi wannan furucin ne a yayin da ya ke ganawa da Kwamitin Ayyuka na kasa na jam'iyyar PDP da suka kai masa ziyara karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar na kasa Prince Uche Secondus don masa jajen rasuwar mutum 8 cikin tawagar Sarkin Kauran Namoda da 'yan bindiga suka kashe.

Ya ce za a ci galaba a kan 'yan bindigan idan dukkan gwamnonin yankin sun hada kai waje guda domin a lalata sansanin 'yan bindigan da ke Jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

"Zamfara ce cibiyar 'yan bindiga a Arewa kuma idan an dauki matakin da ya dace a kan 'yan bindiga a Zamfara, ina tabbatar maka cewa batun hare-haren 'yan bindiga a Arewa zai zo karshe.

"Don haka ina kira ga takwarori na da hukumomin tsaro su saka ido a Jihar Zamfara domin mu gano dukkan sansanin 'yan bindigan mu lalata su.

"Idan ba mu lalata sansanin su ba, ba dole bane mu iya kawo karshen 'yan bindiga a Arewa ko Najeriya. Duk abinda 'yan bindiga za su fada maka yayin sulhu, ya zama dole mu kwace dukkan makaman da ke hannunsu, idan ba muyi hakan ba, ba zamu cimma burinmu ba," in ji shi.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN