Abubuwan da ya kamata ka sani kafin ka nemi auren yar kabilar Ebira


Kabilar Ebira ana samun su ne a jihar Kogi musamman a kananan hukumomi biyar na jihar da suka hada da Okehi, Ajaokuta, Okene, Ogorimagongo da Adavi.

Baya ga jihar Kogi, kabilar sun yadu a fadin wasu jihohin Najeriya musamman a Ondo da Ekiti.

Matan kabilar sun kasance masu tsantsar kyawu kuma cikin sauki hankalin maza ke karkata a kansu. Kyawunsu kadai zai sa mutum ya ji yana kaunarsu a ganin farko.


Sai dai duk da kyawunsu akwai abubuwan da ya kamata ka sani game da su kafin ka auresu. Dalili kuwa shine domin ka shirya kan abunda za a nema daga gareka a lokacin bikin.

Ga wasu daga cikin abubuwan:

1. Mafi akasarin mutanen kabilar Musulmai ne wanda hakan ke nufin yawancin kyawawan yan Ebira da kake gani Musulmai ne wadanda suka riki addini sosai, kuma da wuya a sauya su ta dalilin aure.

2. Idan kana son aure daga kabilar Ebira, ba huruminka bane sanar da iyayenta kudirinka. Yayinda wasu da dama ke tunkarar iyayen yarinya kai tsaye don sanar masu da kudirinsu, a al’adar Ebira, magabatanka ne za su aikata hakan.

3. A yayin baiko wanda ake kira da ‘Ise Ewere’ da yaren Ebira, magabatansa ne za su je gidan surukansu don yin wasu al’ada.

Sannan a yayin baikon, magabatan amaryar za su samar da kayan abinci da na sha domin karrama bakinsu.

A yayin baikon kuma, magabatan angon za su samar da wasu kayayyaki kamar haka:

Doya guda 100

Bushasshen kifi da naman daji

Lemukan sha

Goro

Man ja

Buhun gishiri

Man gyada

Sarkoki na amarya

Tufafin sawa a cikin jaka na amarya

Zanuwa biyu na amarya (ba dole bane)

Kudi na magabata

Wasu daga cikin wadannan kayayyaki ba dole bane bisa ga al’ada saboda ya danganta da ra’ayin yan uwan amaryan. Idan suka ga dama suna iya soke kayayyakin.

Wani abu kuma da za a lura game da kayayyakin shine, ana raba mafi akasarinsu ne ga yan uwa da makwabta domin su sanyawa amaren albarka.

4. Kudin sadaki

Magabatan amarya ne ke yanke kudin sadaki kuma mafi yawan lokuta su kan duba karfi da wadatan angon ne.

Sai dai kuma akwai wasu kudade da wajibi ne a biya su bisa ga al’ada, kamar:

1. OZEMEIYI: Wannan kudi ne da ake biya don tabbatar da cewar angon na muradin amaryar.

2. OTANUVOGE: Wannan shine kudin da ake biya domin hada hannayen ma’auratan a waje daya.

3. IDOZA: A lokutan baya, mutumin da ke son auren yarinya dole ya taimakawa surukansa a gona amma a yanzu, kudi ake biya a madadin haka. Kudin da za a biya saboda haka shine Idoza.

Mun samu wannan cikakken bayani ne a wani wallafa da shafin Arewa RantHQ yayi a Facebook.

A wani labari, Shahrarren attajirin jihar Katsina, Dahiru Mangal, ya bada gudumuwar sama da motoci 100 ga yakin neman zaben tsohon minista, Mohamed Bazou, a jamhurriyar Nijar.

A wani bidiyon da PRNIgeria ta samu, attajirin ya bayar da motocin ne a garin Maradi, wacce ke da iyaka da Najeriya.

An yi rubutu “Mohammed Bazoum, 2021” a jikin motocin hade da hotunan dan takaran.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN