Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati


Tsohon sanata Shehu Sani, ya ce wasu gwamnonin sun fi daraja indomie fiye da rayuwar jama'a.

Ya fadi hakan ne a matsayin martani a kan bin gida-gida da gwamnoni suka umarci jami'an tsaro don kwato kayan abincin da mutane suka sata daga ma'adanar gwamnati.

Idan ba'a manta ba, sakamakon zanga-zangar EndSARS da ta koma rikici, matasa sun balle ma'adanar gwamnati suka yi ta satar kayan abinci.

Kamar yadda wasu bidiyoyi suka bayyana, yawancin matasan, kayan abinci suka yi ta kwasa cikin kwanaki 13.

Bayan faruwar lamarin ne gwamnoni suka umarci hukuma da su bi gida-gida wurin binciko kayan.

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, ya tsoratar da 'yan jiharsa, inda yace zai sa a rushe gidan duk wanda aka kama da kayan tallafin.

A wata wallafa da Shehu Sani yayi a ranar Asabar, yace: "A wurin gwamnoni, indomie ta zama zinari, yayin da rayuwar mutane ta zama azurfa."

Bayan wannan wallafar, mutane da dama sun yi ta tsokaci, suna nuna amincewarsu da maganar sanatan. Ga wasu daga cikin tsokacin:

Wani Gbemi Nath Olorungbon cewa yayi, "Mafi yawan 'yan siyasanmu basu san darajar rayuwar mutane ba sai lokacin zabe."

TheGreatKhalid ya ce, "Gwamnatinmu za ta iya zuwa gida gida don nemo kayan tallafi amma ba za ta iya bin kananun hukumomi ba don raba kayan tallafin."

A wani labari na daban, wata mata ta rasa ranta a daren Litinin yayin damben kwasar kayan tallafin COVID-19 a ma'ajiyar karamar hukumar Kaura dake Kagoro, Daily Trust ta wallafa haka.

Daily Trust sun bayyana yadda mamaciyar, Esther Mba, wacce take da shekaru a kalla 45 ta rasa ranta sakamakon damben dibar kayan tallafin.

Kamar yadda bayanai suka zo, bata-garin sun fara kwasar kayan abincin ne da misalin karfe 7 na daren Litinin, duk da harbe-harben jami'an tsaro da na 'yan sa kai, amma abin ya ci tura.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN