Za mu kashe duk wanda muka gani yana zanga zangan EndSARS a Abuja bayan awa 48 - Matasa


Wani gungun matasamaza da mata da suka kira kansu yan asalin birnin Abuja, sun yi kira ga Safeto janar na yansandan Najeriya IGP ya kawo karshen aikace aikacen masu zanga zangan End SARS a birnin Abuja.

Yayin gabatar da bukatarsu, matasan sun ba IGP awa 48 ya hana kowa zanga zanga a titunan Abuja, sun ce duk wanda ke son ya yi zanga zanga ya koma Kauyensu ya yi zanga zangan.

Sun ce duk wanda suka gani yana zanga zanga bayan awa 48 a Abuja zai fuskanci farmaki, ko ma za su kashe duk wanda ke zanga zangan End SARS a Abuja.


 

Kazalika sun ce da farko sun dauka da kyakkyawar manufa ake zanga zangan End SARS, amma daga bisani sun gano cewa siyasa ne lamarin wanda ke kunshe da boyayyen manufa.

Sun ce zanga zangan ya tauye ayyukan neman abinci da harkokin yau da kullum ga talakawan Abuja.

Mataimakin Safeto janar na yansanda DIG  Leye Oyebade ya tarbi gungun matasan tare da karbar rubutaccen bukatunsu ga IGP. Ya yi alkawarin cewa zai mika takardar ga IGP.

 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN