• Labaran yau


  Yi wa yar shekara 20 fyade: An dakatar da shugaban yansanda da hafsoshi 4 daga aiki

   


  An dakatar da yansanda biyar daga aiki sakamakon sakaci wajen daukan mataki bayan an yi ma wata yarinya yan Dalati fyade a jihar Uttar Pradesh, lamari da ya jawo kasaitaccen zanga zanga a jihar.

  Shugaban yansandan gundumar Hathras, yana cikin yansanda biyar da aka dakatar, domin a gundumar ne aka yi wa yarinyar mai shekara 20 cin zarafi na keta bidurcinta ranar 14 ga watan Satumba a wani fili da ke kauyen.

  Iyayen yarinyar sun ce sun sameta a mawuyacin yanayi cikin jini, kuma tsirara, kuma an yi mata raunuka a bayanta.

  Yarinyar ta mutu a wani Asibiti a birnin Delhi.

  An kama wasu mutane hudu a kauyen dangane da lamarin.

  An dakatar da Vir Vikrant Singh shugaban yansandan gundumar tare da yansanda hudu, bisa zargin rashin kul da aiki ta hanyar rashin sa ido kan ayyukan da yansanda na kasa da shi ke yi.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yi wa yar shekara 20 fyade: An dakatar da shugaban yansanda da hafsoshi 4 daga aiki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama