Yansanda sun kama "Kwamandan shiya" na masu garkuwa da mutane


Yansanda sun yi ram da wani kasurgumin dan fashi kuma mai garkuwa da mutane domin karban kudin fansa mai suna Muhammad Sani dan shekara 30.

Kakakin hukumar yansandan Najeriya DCP Frank Nba ya gabatar wa manema labarai da Muhammad, da ya kira kansa "Kwamandan shiya na masu garkuwa ja jama'a" tare da masu aikata mugan laifuka su 46 ranar Laraba 30 ga watan Satumba. An gabatar wa manema labarai mutanen ne a ofishin yansanda na SARS a birnin Abuja.

Sai dai Muhammad ya ce ya kan saki wadanda ya yi garkuwa da su idan sun biya kudin fansa, wadanda basu biya kudi ba sai ya kashe su.

Ya ce yana da mutum 120 da suke zaman yaransa wajen aikin sace mutane da garkuwa da su. Kuma yakan gudanar da aikinsa ne a jihohin Zamfara, Kaduna, Niger da Katsina, kuma yana yi ma wani mai suna Yellow Jambros aiki ne, domin shi ne yake ba shi Khakin soji, da bindigogi.


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari