Yadda matashi ya yi amfani da kwayan tramadol ya sace Naira miliya shida a wajen dankasuwa


Rundunar yansandan jihar Niger ta kama wani dan fashi da ya shahara wajen amfani da kwaya wajen kwace dukuyar jama'a.

An kama wanda ake zargi mai suna Abdullahi Maikudi dan shekara 27 wanda dan jihar Katsina ne, tare da abokin aikata laifinsa mai suna Rabiu Abdullahi mai shekara 23 dan asalin jihar Kano, bayan sun sace ma wani dan kasuwa kudinsa Naira Miliyan shida a garin Tegina, da ke karamar hukumar Rafi a jihar Niger.

Kakakin hukumar yansandan jihar Niger ASP Biodun ya ce, Maikudi ya kama hayan daki a wani Otel a garin Tegina, inda ya kula da harkar wani dan kasuwa har ya yi abota da shi bayan ya ce masa sun zo daga jiha daya ne.

Daga karshe dai Maikudi ya ba dan kasuwa shayi ba tare da sanin cewa ya sa Kwayar Tramadol a cikin shayin ba. Bayan dan kasuwa ya sha shayin ne, cikin minti 10 sai ya buge da barci. Sakamakon haka sai Maikudi ya shiga dakinsa ya sace jakar kudi da ke dauke da Miliyan shida.

Daga bisani Mikudi ya gudu zuwa Kano inda ya hadu da Rabiu Abdullahi, kuma suka shirya yadda zai gudu ya bar kasar da kudin kafin dubunsu ta cika.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN