Madalla: Gwamnatin jihar Kebbi za ta ba matasa tallafi domin dogaro da kai - Hon Hassan Shalla

Rt. Hon. Hassan Muhammad Shalla


Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya tsaf domin taimaka wa matasan jihar da tallafi bisa sabbin tsare tsare da zai kai matasan ga dogaro da kai ta hanyar wadatar da su da hanyoyin sana'oi da tallafi bisa tsari. Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kebbi Rt. Hon Hassan Muhammad Shalla ya shaida wa Mujallar ISYAKU.COM ranar Alhamis 22 ga watan Oktoba a garin Birnin kebbi.

KALLI BIDIYO 

1. Gwamnatinnjihar Kebbi za ta taimaka wa masu sana'oi da za su iya taimaka ma wasu domin su amfana

2. Wasu tallafin kyauta ne Gwamnati za ta bayar ga masu sana'oi

3. Wasu kuma za a basu tallafi ne amma za a biya kadan daga kudin tallafin domin sauwaka wa al'umma da Gwamnatin jihar Kebbi ta dukufa za ta ci gaba da yi.

Gwamnatin jihar Kebbi za ta koya wa matasa sana'a, kazalika za ta basu tallafin abin da za su ci gaba da yin sana;ar domin su dogara da kansu.

4. Manufar Gwamnatin jihar Kebbi shi ne ta samar da matasa masu dogaro da kai wajen sama wa kansu sana'a ko abin yi domin samun madogaran rayuwa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN