An kama dan shekar 11 cikin batagari da suka wawushe ofishin yansanda


Yansandan jihar Edo sun kama wani yaro mai shekara 11 bisa kasancewarsa cikin wadanda suka kai wa  ofishin yansanda  hari a Uvbuotubu da ke birnin Benin a jihar Edo.

Idan baku manta ba, bata garin sun yi Amfani da zanga zangan EndSars suka farmaki kasuwar Oba, ofishin yansanda na Ugbekun, da na  Idogbo kuma suka yi awon gaba da kayaki da dama har da tufafin yansanda.

Rahotanni sun ce  bayan farmakin, an ga Yaron sanye da rigar Sajen na yansanda  kuma ya ce shi ne Safeto Janar na yansanda.

Kazalika rahotu ya nuna cewa wannan yaro ya yi ta yawo sanye da wannan rigar yansanda a birnin Benin yana barazana da Sabon matsayi da ya ba kansa, sauran yara da jama'a na yi masa shewa.

Tuni yansanda suka cafke shi kuma za a gurfanar da shi a Kotun Yara a cewar rahotun


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN