Zaben Edo: 'Yan daban da ke yi wa PDP aiki sun yiwa matar shugaban jam'iyyar mu duka - APC (Hotuna)


Zaben Edo: APC ta yi ikirarin an yi wa matar shugaban jam'iyyar ta duka, an garzaya da ita asbiti. Hoto daga Edo State APC Source: Twitter Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Edo ta yi ikirarin cewa 'yan daba da ke yi wa jam'iyyarPeoples Democratic Party (PDP) aiki sun yi wa matar shugaban ta na Egor duka.


Jam'iyyar ta APC ta yi ikirarin cewa an mata duka ne saboda ta yi jayayya da 'yan daban da suka zo rumfan zaben da nufin tada tarzoma kamar yadda The Nation ta ruwaito.


A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter @EdoStateAPC, jam'iyyar ta saka hotuna masu yawa na matar da ake yi wa duka a lokacin da wasu ma'aikatan jinyar asibiti ke mata magani. Sakon ta suka wallafa a Twitter ya ce: " Yan daban @OffcialPDPNig sun kwace kayyakin zabe a rumfar zabe ta Tipper Garage da ke Egor.


Matar shugaban jam'iyyar mu ta yi kokarin hana su amma suka mata mugun duka. An garzaya da ita zuwa asibiti mafi kusa." Majiyar Legit.ng Hausa ba ta tabbatar da inda asibitin ya ke ba.

Seniora: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN