Yadda shugabannin kananan hukumomi 2 suka ba hammata iska a bainar jama'a a jihar Niger

 


Rahotanni sun kawo cewa rigima ta kaure a tsakanin Shugaban karamar hukumar Suleja , Alhaji Abdullahi Maji, da na karamar hukumar Gurara, Mista Yussuf Wali Gwamna, kan shugabancin kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Niger. Wannan labari har ya kai su ga ba hammata iska a bainar taro, jaridar Leadership ta ruwaito.


An tattaro cewa dukkaninsu su biyu sun nuna ra’ayinsu na neman kujerar shugabancin kungiyar, sannan kowannensu ya ki hakura ya janye wa dan uwansa takarar. Rahoton ya nuna cewa ana cikin haka ne, sai Wali Gwamna na karamar hukumar Gurara ya lakada wa Maji mugun duka wanda har sai da ya kai ga ya suma, inda aka kwashe shi zuwa wani asibitin kudi don jinyan raunukan da ya samu.


Majiyoyi a wajen taron na wanda aka gudanar a Kaduna, sun ce an fara samun matsala ne a lokacin da aka nemi wakilan Jihar Neja da su jagoranci tawagar jihar zuwa Zariya. Za su Zariya ne domin yi wa Masarautar Zazzau ta’aziyyar rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris. Toh a nan ne sai shugaban karamar hukumar ta Suleja ya gabatar da kansa a matsayin shigaban kungiyar daga Jihar.


Don haka sai Wali Gwamna wanda ya nuna fusatarsa a fili kan ikirarin Maji, ya musanta cewa shi (Maji) ne shugabansu. A kokarin da yayi na nuna bacin ransa ne bayan da tawagar ta wuce zuwa Zariya, shine ya kai sa ga lakada wa shugaban na karamar hukumar ta Suleja mugun duka.


Majiyoyin sun ce damben ya kai ga lalata dukkanin abin da ke kan saman teburin taron da kujeru sannan suka farfasa duk sauran kayayyakin. An ce shugabannin biyu sun ja junansu ne zuwa tsakiyar dakin taron, inda suka fara dambe kafin sauran shugabannin kananan hukumomin da suke a wajen su shiga tsakani.


Mai ba gwamnan jihar Niger shawara a kan harkokin siyasa, Alhaji Nma Kolo, ya tabbatar da afkuwar lamarin. Ya ce gwamnatin jihar na bincike a cikin lamarin. Kolo ya kuma bayyana cewa, shugabannin biyu sun kunyata jiharsu A wani labari na daban, mun ji cewa wasu fusatattun matasa a ranar Talata sun kai wa hadimin gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar da wasu jami'an gwamnatin jihar hari

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN