Masarautar Zuru: Kalubalen tsaro, sabon alkibla da muhimmin ababen da ya kamata ka sani


Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi ta gudanar da taron koli kan harkar tsaro ranar  Asabar 12 ga watan Satumba domin ci wa matsaya tare da fadakar da wadanda aikin tafiyar da tsaron ta hanyar sa kai ya shafa, tare da sauran al'umman Masarautar.

 

Wannan yana zuwa ne bayan Masarautar Zuru ta yi ta fama da matsalolin tabarbarewar tsaro sakamakon kutse zuwa kasar Zuru da ake zargin wasu batagari suka yi bayan tsananin barin wutan jami'an tsaro a jihar Zamfara ya sa suka yi kaura zuwa yanki na Zuru da ke jihar Kebbi.

 

Sakamakon  kalubale ga tsaro a Masarautar Zuru, lamarin ya kai ga kisan wani basaraken gargajiya na garin Bajida fiye da wata daya da makonni da suka gabata, bayan lamurran tabarbarewar tsaro da ake zargin sun ci gaba da kunno kai a Masarautar Zuru.

 

Masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Masarautar Zuru da jihar Kebbi, sun tashi tsaye, kuma suka dukufa wajen ganin an daidaita tsarin tafiyar da yadda za a gudanar  da tsaro a Masarautar Zuru bisa karbabben yanayi na bin doka da oda, marmakin daukan doka a hannu wajen da'awan tafiyar da harkar tsaro daga wadanda aikin yin haka ya shafa. Daga cikin alkiblar da aka fuskanta bisa jawabin masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro, har da shirin tura yan sa kai domin su sami horo na musamman, da kuma gargadi tare da hani kan daukar doka a hannu ta hanyar zartar da hukunci ba tare da bin yardadden ka'idodin doka ba.

 

Taron, wadanda aka gudanar a babban dakin taro na garin Zuru, ya sami halarcin manyan tsofaffin jami'an tsaro masu murabus, wadanda suka hada da babban kwamandan askarawan sojin kasa na Najeriya, kuma babban Janar na sojin kasa a jihar Kebbi da ya yi ritaya da mukamin Janar mai tauraro uku, Janar Ishaya Bamayi, da Janar mai  tauraro biyu, Manjo Janar, Mai martaba Sarkin Zuru Muhammadu Sani Sami Gomo na 2, da Janar mai tauraro biyu kuma tsohon Minista a zamanin mulkin soji, Manjo Janar Muhammadu Magoro da kuma Mataimakon Gwamnan jihar Kebbi Kanar Samaila Yombe Dabai, tare da sauran tsofaffin jami'an tsaro masu murabus.


Haka zalika taron ya sami halarcin sashen tsaro na Gwamnatin jihar Kebbi, wadanda suka hada da Alhaji Rabi'u Kamba. Tare da Sakataren din din dim kan harkar tsaro a jihar Kebbi, Alhaji Sufiyanu Bena, da Darakta kan harkar tsaro na Gwamnatin jihar Kebbi.


Sauran sun hada da manyan yan siyasar Masarautar Zuru, Sanata Bala Ibn Na'Allah, Dan Majalisar tarayya Kabiru Tukura na daga cikin wadanda suka halarci taron na ranar Asabar, tare da dimbin jama'a maza da mata daga sassa daban daban na rauwa a ciki da wajen garin Zuru.

 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN