Kuma dai: An sake sace jami'in DSS, an nemi N100m a matsayin kudin fansa (Hotuna)


'Yan bindiga sun sace jami'in hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS, tare da dansa mai shekaru hudu a ranar Asabar a jihar Kaduna. Jami'in da a yanzu ba a bayyana sunansa ba ya fada hannun masu garkuwar ne a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a ranar Litinin kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito. Rahotanni sun ce yan bindigan sun tuntubi iyalansa sun nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan 100 kafin su sako shi.Jami'in da aka yi garkuwa da shi yana aiki ne a matsayin mai kula da inda ake ajiye makamai na makarantar horas da sabbin jami'an DSS. Hakan na zuwa ne awanni kadan bayan yan bindiga sun kashe wani jami'in DSS mai shekaru 33 mai suna Sadiq Abdullahi Bindawa duk da kudin fansa Naira miliyan 5 da aka biya.


Marigayi Bindawa yana gidansa ne da ke bayan sakatariyar gwamnatin tarayya a Katsina yayin da yan bindigan suka kai masa hari. Bindawa yana aiki ne da sashin tattara bayannan sirri na hukumar da ke Abuja. Kamar yadda lamarin ya ke a wasu sassan kasar nan, ana samun hare haren 'yan bindiga da garkuwa da mutane a jihohin Kaduna da Katsina a cikin makonnin da suka gabata. 

A wani rahoton, kun ji cewa daya daga cikin manyan mambobin kungiyar ƴan daba ta marigayi Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana wanda ya ce sunansa 'Manjo' ya ce za su cigaba da gwagwarmaya duk da shugabansu ya mutu. Ya ce marigayi Gana ya ji a jikinsa cewa zai mutu hakan yasa ya mika shugabancin ga wanda ke biye masa a ƙungiyar sa kafin zuwa rungumar shirin afuwa filin motsa jiki na Atongo a Katsina-Ala.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN