• Labaran yau


  Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe


   

  Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a gidan gwamnati a babban birnin tarayya Abuja.


  Wannan shine ziyara ta farko da Obaseki ya kai wa Buhari bayan lashe zaben gwamna karo na biyu a jihar Edo a ranar Asabar da ta gabata. Obaseki ya lashe zabensa na farko ne a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, amma daga bisani ya sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, inda ya sake lashe zaben karo na biyu. Mataimakinsa, Mista Philip Shuaibu ya raka Obaseki zuwa fadar shugaban kasar.


  Wasu daga cikin 'yan majalisa da iyalan Obaseki da Philip suma sun musu rakiya a ziyarar da suka ce sun kai wa shugaban kasar don yi masa godiya. 

  A cikin sanarwar da jam'iyyar ta fitar, sakataren watsa labarai, Ade Ajayi ya ce tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Omotune Ojo yana cikin wadanda aka dakatar. 

   

  Ojo surukin Bola Tinubu ne, jagora na kasa na jam'iyyar ta APC mai mulki. Ajayi ya ce an dakatar da mambobin jam'iyyar ne saboda kin janye karar da suka kai jam'iyyar a kotu.   Ga hotunan ziyarar a kasa:    Source: Legit
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama