Daidaicewar Najeriya: Buhari da ACF sun yi wa Obasanjo martani mai zafi


Wani babban jami'i a fadar shugaban kasa ya gaggauta yi wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, martani a kan ikirarinsa na daidaicewar Najeriya karkashin mulkin shugaban kasa Buhari. Duk da babban mai bai wa shugaban kasar shawarana musamman a fannin yada labarai, Garba Shehu, bai yi martani ba, babban jami'in wanda bai bukaci a bayyana sunansa ba, ya kwatanta Obasanjo da mutumin da.



Ya ce: "Obasanjo mutumin da ne. Ya yi suka ga shugaba Buhari kuma ya ci zabe, ba za a taba tsammanin cewa zai taba yabonsa ba." Obasanjo a ranar Alhamis ya ce a hankali Najeriya take tabarbarewa tare da daidaicewa a karkashin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta wallafa. A yayin martani ga tsokacin Obasanjo, shugaban kungiyar 'yan arewa kuma tsohon ministan noma, Audu Ogbeh, a wata tattaunawa da yayi da Daily Trust a ranar Lahadi, ya ce wannan rashin dattako ne.



Ya ce: "Bayyana tabarbarewar Najeriya rashin dattako ne. Bari in sanar da wani abu, yana da nashi kalubalen a tattare da shi. Ina Zaki Biam da Odi? Babu wanda yace maka ka isa ka duba yadda wasu shugabanni ke aiki." A yayin tunatar da Obasanjo, Ogbeh wanda tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne zamanin mulkin Obsanjo, ya ce: "Ina tunanin idan da Gowon, Abdulsalami da Shagari sun cigaba da caccakar shugabanni, babu wanda zai ga mutuncinsu. "Ina tunanin yana jin dadin abinda yake yi. Yana neman a sauraresa kuma a yaba masa a kan miyagun maganganunsa."



A yayin tabbatar da cewa Najeriya tana da matsala kuma dole a shawo kanta, Ogbeh ya ce: "Ina mutunta Obasanjo, yana da kaifin basira amma ya gujewa kalubale mara tushe." Idan za mu tuna, tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya sake sukar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari inda ya ce ƙasar ta kama hanyar lalacewa kuma kawunnan yan kasar sun rabu. Obasanjo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a wurin wani taron da kungiyoyi masu wakiltan yankunan kasar suka hallarta.

Source: Legit



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN