Da duminsa: An kaiwa tawagar Adam Oshiomole hari, mutane da yawa sun mutu

Jam'iyyar APC, ta dagakatar da gangamin yakin neman zabenta a jihar Edo sakamakon wani hatsari da ya rutsa da tawagar manyan shuwagabannin jam'iyyar, ciki har da tsohon shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole. A shafinta na Twitter, APC ta yi ikirarin cewa, hatsarin ya faru ne da gangan, ana so ne a kashe manyan jagororin jam'iyyar.

Dan takarar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyar ta APC, Pastor Osagie Ize-Iyamu, ya soke gangamin yakin zaben da za a yi a Usen, sakamakon wannan hatsarin. Kafin sha tale talen Oluku, wata babbar tirela ta bi ta kan motocin tawagar yakin zaben, da ke dauke da jagororin jam'iyyar, lamarin da ya jawo asarar rayuka.

A cikin wata sanarwa daga shugaban sashen watsa labarai na kungiyar yakin zaben gwamnan jihar na jam'iyyar, Mr. John Mayaki, ya ce an soke taron ne don jimamin wadanda suka mutu. A madadin Pastor Ize-Iyamu da jam'iyyar APC, Mayaki ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, yana mai cewa ba su kaine ke bakin ciki ba.

Ya ce kungiyar yakin zaben za ta yi duk mai yiyuwa a iya karfinta wajen ganin ta saukaka masu radadin rashin da suka yi. Da ya ke mika sakon ta'aziyya ga iyalan 'yan sandan da suka rasa rayukansu, ya ce jihar Edo ba za ta taba mantawa da sadaukarwar da suka yi ba. Sanarwar ta yi kira ga daukacin al'umma da su ci gaba da yin addu'a ga wadanda suka rasa rayukansu, da kuma rokon Allah ya kare faruwar hakan a nan gaba.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN