Yan aware sun sare wuyar uwar yara 4 bayan sun daure hannayenta a bayanta a Cameroun

Kungiyar kula da hakkin bil'adama ta Duniya Human Rights Watch (HRW) ta yi Allah wadai da kisa da wasu yan aware suka yi ma wata mata mai suna  Confort Tumassang mai shekara 35 kuma mahaifiyar yara hudu.

Wani faifen bidiyo da ya dinga zagayawa a intanet, ya nuna yadda wasu yan aware masu tayar da kayar baya a garin Muyuka da ke yankin Arewa maso Gabacin kasar Cameroun suka daure hannayen matar a bayanta, suka daure wuyarta da igiya, daga bisani suka sare kanta da Adda a yanayin tashin hankali

A wani rahotu da ta fitar, HRW ta ce ba wannan ne karon farko da yan awaren ke aikata irin wannan kashe-kashe na rashin imani ba a yankin Arewa maso gabacin kasar Camaroun, kuma ta yi Allah wadai da matakin da yan awaren ke daukawa na kisan gilla ga bayin Allah.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN