Domin idanuna da na yara na su 2 launin shudi ne mijina ya yi watsi da mu a Duniya

Wata mata mai suna Risikat Azeez-Ayegbami mahaifiyar yara biyu dukkansu masu shudin idanu, ta ce mijinta ya yi watsi da ita tare da yaranta mata guida biyu kawai domin suna da shudin idanu.

'Yar asalin jihar Kwara, ta ce, an haifeta ne da wannan launin ido. Ta ce haka zalika iyayenta sun sha fama da ita wajen zuwa asibitoci domin yin gwaji, amma sakamakon gwaji na nuna cewa idanunta lafiya kalau suke.

Ta ce hatta lokacin da take 'yar karama, bayan iyayenta sun kai ta asibiti domin gwaji, daga bisani Likitoci sukan kirata domin a cewarsu launin idanunta na birge su, kuma har kyautuka suke bata.

Risikat ta ce, mijinta ya yi sha'awarta duk da launin idanunta, kuma suka yi aure. Ta ce bayan ta haifi diyarsu ta farko ita ma dauke da idanu masu launin shudi, sai mijinta ya fara tsananta, yana kaurace wa yin magana da ita.

Ta kara da cewa lamari ya canja  ne tsakaninta da mijinta bayan ta sake hauhuwar diyarsu ta biyu amma ita ma tana da idanu masu launin shudi.

Sakamakon haka mijinta ya canja yanayinsa ga iyalinsa hatta abinci yana gagaransu a yini. Ta ce sakamakon haka, take zuwa gidan iyayenta domin ta ci abinci. Daga bisani a cewarta, mijinta ya yi watsi da ita tare da yaranta mata guda biyu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN