Yadda mahaifi mai yara 8 ya banka wa yarshi mai shekara 16 cikin gaba da fatiha

Legit

Rundunar Yan sandan jihar Yobe ta yi holen wani mutum mai shekara 43 da ke da yara takwas da aka ce ya yi wa ƴar cikinsa mai shekara 16 ciki a Damaturu babban birnin jihar.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Juma'a, Kakakin Rundunar 'Yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ya ce wanda ake zargin ya saki matarsa shekaru biyar da suka gabata kuma bai sake aure ba. Wacce abin ya faru da ita, wadda yanzu ta ke dauke da juna biyu na watanni shida ta ce mahaifinta ya fara lalata da ita tun a shekarar 2015.

A wani labarin mara dadin ji mai kama da wannan, wani da ake zargi kuma kurma ya yi lalata da wani karamin yaro mai shekara takwas. Mahaifin wanda abin ya faru da shi ya ce lamarin ya faru ne a garin Damaturu inda wanda ake zargin ya shigar da yaronsa cikin masallaci kuma a lokacin da aka kama shi zai ya wayince kamar salla ya ke yi.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji Rundunar 'Yan sanda a jihar Abia ta kama wata Mrs Rose Uwaga a kan zargin sheke mijinta mai shekara 83, Alhaji Isa Uwaga a Umuahia babban birnin jihar. Kakakin rundunar ta jihar, Geoffrey Ogbonnaya ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, kama matar mai shekaru 73 a garin Umuahia a ranar Laraba. Ogbonnaya ya ce daya daga cikin yayan Uwaga, Ibeabuchi, ne ya kai wa 'yan sanda rahoto a kan lamarin a ranar 2 ga watan Yuli.

Ya ce gawar mamacin tana dakin ajiye gawa na asibiti "inda ake sa ran gudanar da bincike a kan ta don sanin anihin abinda ya kashe mutumin." NAN ta gano cewar ma'auratan sun samu rashin jituwa har ta kai ga dambacewa a gidan su da ke Ohobo-Afara Umuahia.

"Yayin fadar, mutumin ya dakko adda domin ya firgita matar amma ta fi karfinsa ta murde hannunsa. "Addar ta fadi daga hannunsa kuma matar da ke da girman jiki ta danne shi a kasa ta shake masa wuya har sai da ya mutu," a cewar wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post