Duba muhimman ababe 3 da suka faru a Najeriya a mako da ya gabata

Rahotun  Legit

A yau Lahadi, 12 ga watan Yulin 2020, Legit.ng ta zakulo wasu muhimman ababe da suka wakana a kasar nan cikin makon jiya.

Jigo cikin manyan al'amuran da suka karade dandalai da zaurukan sada zumunta kuma har yanzu suna gudana kan harsunan al'umma, shi ne titsiyar da ake yi wa Ibrahim Magu.

Sauran ababen da suka faru a makon jiya sun hadar da yadda ake kai ruwa rana kan sha'anin siyasa musamman dangane da zaben gwamnan Edo da na Ondo da za a gudanar a watan Satumba da kuma mai bi masa wato Oktoba.

Akwai kuma batun rattaba hannu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kan kasafin kudin kasar nan na bana da aka yi wa kwakwarima.

Badakar Magu:

A ranar Talata ne dai fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim Magu daga jagorancin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar nan ta'annati.

Wata majiya mai karfi da ta bukaci a sakaya sunanta wadda ta fito daga fadar shugaban kasa, ita ce ta bayar da tabbas a kan wannan rahoto.

Hukuncin da fadar shugaban kasar ta dauka ya biyo bayan bayyanar Magu a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba. Kwamitin wanda ke karkashin jagorancin tsohon mai shari'a Ayo Salami, ya gayyaci Magu ne domin jin ta bakinsa kan abubuwan da suka shafi jagorancinsa a hukumar ta EFCC.

Har kawo yanzu, Magu dai yana can tsare a hannun kwamitin, inda ake ci gaba da titsiye shi tare da tatso bayanai daga garesa a yayin neman samun tabbaci kan zargin almundahana da dukiyar kasa da ake tuhumarsa.


Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin bana da aka yi wa kwaskwarima:


Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya saka hannu a kan kasafin kudin shekarar 2020 da aka yi wa kwaskwarima. Tolu Ogunlesi, hadimi na musamman a kan sabuwar hanyar sadarwa ga shugaban kasar, ya wallafa cewa,

Buhari ya sanya hannu a kan gyararren kasafin kudin da misalin karfe 11.04 na safiyar ranar Juma'a. Tun a ranar Alhamis ne dai Ministar Kudi, kasafi da tsare-tsaren ci gaban kasa; Zainab Ahmed ta shaidawa majalisar dokokin tarayya cewa Buhari zai rattaba hannu a kan kasafin kudin da aka yi wa kwaskwarima a ranar Juma'a.

 An yi wa kasafin kudin kwaskwarima ne bayan faduwar farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya da kuma bullar annobar korona da ta janyo tsaiko a kan hada hadar kasuwanci a duniya.


Zaben Gwamnan Ondo:

Jam'iyyu 17 sun sanar da INEC kudirinsu na gudanar da zaben fidda gwanin takara Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta sanar da cewa, daga cikin jam'iyyu 18 masu lasisi, 17 sun tabbatar da mata da shirinsu na aiwatar da zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Ondo.

Za a gudanar da zaben ne a ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba na 2020. Hukumar INEC ta sanar da cewa, an wallafa duk wasu bayanai dangane da jam'iyyun da za su fafata a zabe a shafinta na yanar gizo da kuma na dandalin sada zumunta.

Haka kuma hukumar ta sanar da cewa, za a gudanar da zaben gwamnan Edo a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, a yayin da tuni jam'iyyu 14 sun kammala zabukansu na fidda gwanin takara. INEC ta tunatar da jam'iyyun cewa, kamar yadda ta fidda tsare-tsare da jadawalin gudanar da zabe, kowace jam'iyya ta tabbatar ta kammala yakin neman zabenta a tsakanin ranar 21 ga watan Yuli zuwa 17 ga watan Satumba.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN